Cinikin Neymar na Fam miliyan 198 da zai sa ya koma Paris-St Germain bai yi tsada ba, amman zai janyo matsala, in ji Jose Mourinho.
Dan wasan tawagar Brazil din, mai shekara 25, ya shaida wa Barcelona cewar yana son ya bar ta a ranar Laraba.
Kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya soki cinikin bisa ka’idar kudin sayen ‘yan wasa ta hukumar kwallon kafa ta Turai, UEFA.
Klopp ya ce: “Ina tunanin an kafa dokar ne saboda a hana aukuwar irin wannan lamarin. Amman wannan ya fi kama da shawara fiye da doka.”
Cinikin Neymar zai dara na Paul Pogba da ya kafa tarihi a matsayin dan wasa mafi tsada a duniya da kudi fiye da Fam miliyan 100 a lokacin da ya koma Manchester United daga Juventus.
Mourinho ya ce: “Masu tsada su ne wadanda suka kai ga wani mataki ba tare da wasu ire-iren kwarewa ba. A kan kudi fam miliyan 200, ba na tunanin Neymar yana da tsada”.
“Ina ganin yana da tsada kan cewar a yanzu za a iya samun karin ‘yan wasa kan kudi fam miliyan 100, za a samu karin ‘yan wasa kan Fam miliyan 80 da kuma karin ‘yan wasa kan Fam miliyan 60. Kuma ina ganin wanna ita ce matsalar.”
Ya kara da cewar : “Neymar daya ne daga cikin ‘yan wasan da suka fi kwarewa a duniya, yana da daraja a kasuwa, kuma lallai PSG ta yi tunanin hakan.
“Saboda haka ina ganin matsalar ba ta tsadar Neymar ba ce, ina tunanin matsalar ta tasirin Neymar ce.”
Souce In Bbchausa
Add Comment