Kannywood

Cinema: Fim Din Makota Ya Hada Naira Miliyan 1 Da Dubu Dari 1

Fim din MAƘOTA ya haɗa kuɗi Naira Miliyan Ɗaya da Dubu Casa’in da Biyar (₦1,095,000) a kwanakin sa uku na karshen makon sa na farko.

Bayan farawa da rashin kasuwa da fim din MAƘOTA yayi a ranar juma’a da aka sakeshi fim din ya shiga sahun finafinan da suka haɗa Milyan daya acikin kwana uku rak, wanan ya samu ne sanadiyyar karin kudin Ticket din shiga sinimar da akayi (daga ₦1000 zuwa ₦1,500).

Zamu ga ko ragowar kwanakin sa na sati fim din zai motsa yadda ya kamata, tunda ya samu yabo dai-dai gwargwado a bakin yan kallo, duk dadai wasu sun kushe amma masu yabon sunfi rinjaye.

Lokaci zai tabbatar mana da wacce irin kasuwa MAƘOTA zayyi, ko zai iya kamo fim din JARUMA?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: