Labarai

Cin Barcelona ya tayar da kura a Spaniya

Wannan shi ne karo na 4 da ake cin Barcelona 4-0 a gasar Zakarun Turai
Barcelona na kan hanyar kasa kaiwa wasan dab da na kusa da karshe na cin Kofin Zakarun Turai, a karon farko tun 2007, bayan da PSG, ta casa su 4-0, lamarin da ya tayar da hankali a Spaniya. 
Bayan yadda PSG ta taka musu leda, yawancin nazarin da aka yi na yadda wasan ya gudana, ya mayar da hankali ne kan, yadda Barcelona ta yi sakaci, inda galibi ake kakkausar suka kan kociyansu Luis Enrique.
Alkaluman wasan kadai sun isa su nuna yadda aka mamaye Barcelona a wasan: PSG ta kai hare-hare kwarara guda 10, sabanin guda daya kacal da Barca ta kai.
Sannan ‘yan wasan kungiyar ta Faransa sun yi zirga-zirgar da ta kai ta nisan kilomita sama da 112.1, yayin da takwarorinsu na Barcelona suka yi ta kilomita 104.
Haka kuma Zakarun na Faransa sun fi kokarin kwato kwallo, inda suka yi hakan sau 46, su kuwa Zakarun Spaniya sau 36 suka kwaci kwallo.
Hatta shi kansa Lionel Messi ma wanda shi ne gwanin fitar da kungiyar tasa kunya a yawancin lokaci, ya kasa tabuka komai, inda ya kasa ko taba kwallon a da’irar gidan PSG.
Ga kungiya irin Brcelona wadda galibi aka sa rai za ta yi nasara a wasan, a ce ta yi wannan abin kunya, to fa ba abu ne da zai wuce ba haka ba tare da wani abu ya biyo baya ba.
Kila a ce ta riga ta faru ta kare kenan ga kungiyar a wannan gasa ta bana, to amma kurar da lamarin zai tayar yanzu ta fara.