Labarai

China za Ta haramta amfani da mota mai amfani da fetir

Kasar da aka fi cinikin motoci a duniya wato China, na shirin haramta kerawa da kuma sayar da motocin da suke amfani da man fetir da dizal.

Mataimakin ministan masana’antu na kasar ya ce, tuni suka fara nazari na tsanaki, sai dai har yanzu ba su yanke shawarar lokacin da za a tabbatar da haramtawar ba.

 

Xin Guobin ya shaida wa kamfanin dillanci labarai na kasar cewa, “Wadannan matakai za su kawo sauyi wajen bunkasa kamfanonin motocinmu”.

China ta kera mota miliyan 28 a bara, kusan kashi uku na motocin da aka kera a duniya.

Tuni kasashen Birtaniya da Faransa suka sanar da shirin haramta amfani da motocin masu amfani da wutar lantarki da dizal a shekaarr 2040, a kokarinsu na rage gurbatacciyar iska.

A watan Yuli ne kamfanin kera motoci na Volvo ya ce, daga shekarar 2019 duk sabbin motocin da kamfaninsa zai kera masu amfani da wutar lantarki ne.

Geely shi ne mai kamfanin Volvo, kuma a shekarar 2025 ne yake burin sayar da motoci masu amfani da wutar lantarki har miliyan daya.

Wasu kamfanonin motoci da suka hada da Renault-Nissan, da Ford da kuma General Motors dukkaninsu na aikin samar da motoci masu aiki da wutar lantarki a China.

Kamfanonin kera motoci sun fara fafutukar yadda za su bunkasa kasuwar kasar, wajen gabatar da sabbin dokokin da za su yi yaki da gurbatacciyar iska.

Kudirin na bukatar kaso takwas cikin dari na masu kera motocin sayarwa batirinsu ya zama na lantarki ko wanda za a jona a wata motar zuwa shekara mai zuwa, wanda zai karu da kaso 12 cikin 100 a 2020.

Xin ya yi hasashen cewa sauyin zai kawo ce-ce-kuce a masana’antar.

Har ila yau hakan zai kawo karshen yawan bukatar mai a kasar, inda a yanzu kasar ce ta biyu a duniya da take sayen man fetir bayan Amurka.

 

Souce In Mikiya