-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Chelsea Ta Ci gaba Da Zama Ta Hudu A Teburin Premier


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Chelsea ta yi nasarar doke Brighton & Hove Albion 2-1 a gasar Premier wasan mako na 17 da suka fafata a ranar Lahadi.

Chelsea ta ci kwallayen ne ta hannun Pedro minti 17 da fara wasa, sannan Hazard ya ci na biyu a minti na 33 da take-leda, inda Brighton ta zare daya ta hannun March.

Da wannan sakamakon Chelsea ta ci gaba da zama ta hudu a kan teburin Premier da maki 37.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 54

- Advertisement -

Kungiyar ta Stamford Bridge ta yi nasara a karawa 11 da canjaras hudu aka doke ta wasa biyu, sannan ta ci kwallo 35 aka zura mata 13 a raga a wasa 17 da ta yi a Premier.

Chelsea za ta karbi bakuncin Leicester City a ranar 22 ga watan Disamba a wasan mako na 18 da za su kece raini a Stamford Bridge.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: