Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta bayyana sunayen masu horas wa guda biyu da take ganin zasu maye gurbin mai horas warsu na yanzu wato Sarri idan har sakamakon wasanni basu canja ba a kungiyar.
An bayyana sunan tsohon kocin Real Madrid Zinedine Zidane da kuma tsohon dan wasan na Chelsea wato Frank Lampard a matsayin wadanda Chelsea take zawarci idan har ta tabbata Sarri bazai iya ba.
Chelsea tasha fama da rashin nasara a wasannin ta na baya bayannan, ciki kuwa harda wasan da suka yi rashin nasara a hannun Manchester United har gida daci 2 da nema a gasar cin kofin F.A cup.
A wannan wasa da Chelsea ta yi rashin nasara anji magoya bayan na Chelsea sun hada baki da takwarorinsu na Manchester United suna rera waka tare a lokacin da ake gudanar da wasan na F.A cup, wakar na nuni da cewa sun gaji da mai horas war.
- Advertisement -
Zidane, wanda yabar aikin koyar da ‘yan wasan Real Madrid a shekarar data gabata kwanaki kadan bayan ya jagoranci kungiyar ta lashe gasar cin kofin zakarun turai karo na uku a jere a hannun kungiyar Liberpool.
Lampard, wanda tsohon dan wasa Chelsea ne kuma ya lashe kofin firimiya guda biyu da Chelsea da kofin zakarun turai sannan kuma kawo yanzu shine kociyan kungiyar kwallon kafa ta Derby County dake kasar Ingila.
#Hausaleadership