Kakakin rundunar sojin Najeriya, Janar Sani Usman ya ce rundunar sojin bata ji dadi ba saurin sanarwa mutanen Najeriya cewa dakarunta sun ceto ma’aikatan kamfanin NNPC da suke aikin nemo danyar mai a yankin jihar Barno da yayi iyaka da Chadi.
Janar Sani ya ce rundunar batayi haka ba don ta burge, cewa anyi ne cikin kuskure.
Ya bada bayanai kan nasarorin da dakarun sojin dake fafatawa da Boko Haram suka samu tun bayan wannan hari.
“Sakamakon binciken da a ke yi an gano karin gawawwakin wasu sojoji 5, da sojin sa kai wato ‘yan banga 11 da na injiniyoyin dake binciken guda 5.
” Har yanzu ba a san inda mutane shida cikin ma’aikata 12 da suke aikin binciken man ba, amma daya daga cikin ma’aikacin kamfanin NNPC ya tsira da ransa”.
Bayan haka kuma Janar Sani ya ce an samu nasarar kwato bindigogi, motoci, bama-bamai, harsashai, tayoyi, jarkokin man fetur, kwari da baka da na’urorar gudanar da binciken na kimiyyar zamani da hangen nesa.
Ya kara da cewa rundunar sojin na ci gaba da neman maboyar da aka ajiye sauran ma’aikatan da injiniyoyin da je aiki a wurin sannan kuma ya gode wa mutanen ya kin da abin ya faru kan irin gudunmawar da suke ba sojojin.
Idan ba manta ba gidan jaridar Premium Times ta ba da rahoton cewa ba kamar yadda rundunar sojin ta sanar ba, babu ko mutum daya da a ka ceto. Sannan ta bada bayanai kan yadda akayi ta shigowa da gawawwaki asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri.
Source Premiumtimes Hausa
Add Comment