Hukumomi a birnin Lagos da ke kudancin Najeriya sun ce sun ceto ‘yan makarantar da aka sace a birnin.
A watan Mayu ne dai wasu ‘yan bindiga suka sace ‘yan makaranta guda shida.
‘Yan bindigan sun kai hari ne a makarantar Igbonla Model School, inda suka tafi da dalibai guda 10.
Amma rahotanni sun ce sun saki hudu daga cikinsu, bayan da suka binciki asalin iyayensu.
‘Yan sanda sun ce ‘yan bindigar sun samu shiga makarantar ta cikin wani daji da ke gefen makarantar ne, inda suka yanka wayar da ta zagaye makarantar kana suka shiga ciki.
Add Comment