Labarai

CBN ya fitar da sabbin manufofin kudin kasashen waje

Gwamnan CBN Godwin Emefiele ya ce za a tabbatar masu bukatar dalar sun same ta a bankuna kai-tsaye
Babban bankin Najeriya, CBN, ya sanar da cewa ya fitar da wadansu sababbin manufofin musayar kudaden waje.
A karkashin sabon tsarin, Babban Bankin ya ce zai kara yawan kudaden wajen da ya ke bai wa banunan kasar da nufin saukakawa ‘yan Najeriya masu bukatar zuwa asibiti a wasu kasashen, da masu karatu a wasu kasashen da kuma ‘yan kasuwa.
A wata sanarwa da ya fitar, CBN ya ce yana sa ran bankunan za su dinga sayar wa jama’a kudin a kan farashin da bai dara kashi ashirin cikin dari na farashin da bankuna ke musaya a tsakaninus ba, wato Naira 315 a kan ko wacce dala.
CBN ya kuma ce ya dage dokar cewa kashi sittin cikin dari na kudaden kasashen wajen su tafi ga ma’sana’antu, yayin da sauran kashi 40 din ne kawai za a rarraba ga masu tafiye-tafiye da ‘yan makaranta.
Ya kuma ce wannan mataki zai fara aiki ne ba tare da bata lokaci ba.
Alawus din matafiya
CBN ya ce ba tare da bata lokaci ba zai bai wa bankunan kasar domin su sayar wa masu bukatar yin tafiye-tafiye na kasuwanci ko na kashin kai.
Ya ce ko wanne banki za a ba shi iya adadin kudaden kasashen wajen da yake bukata ne a duk mako.
Kudin makaranta da na asibiti
Haka kuma, babban bankin ya ce zai bai wa iyaye da ‘yan makaranta damar samun kudaden wajen a saukake, domin su biya kudin karatunsu.
Sai dai ya ce ba za a dinga ba su kudin kai-tsaye ba, za su bayar da lambar asusun makarantun da suke karatu ne sai bankin da mutum ke hulda da shi ya tura abin da ake bukata kai tsaye.
CBN ya ce zai tabbatar ba a samu wata matsala ba wajen aika kudin, kuma zai yi iya kokarinsa don ganin duk masu bukatar kudaden kasashen wajen sun samu abin da suke so.
Wannan tsari ya kuma shafi masu son biyan kudin asibiti, inda su ma za su bayar da bayanin asibitin da za a tura kudin kai tsaye ba tare da ya bi ta hannunsu ba.
‘Sayar da kudin waje a filin jirgi’
A kokarinsa na rage wahalhalun da matafiya ke sha, da kuma tabbatar da cewa an samu sauki a farashin da ake sayar da kudin kasashen waje, CBN ya kuma umarci dukkan bankuna su bude rassa na sayar da kudin a manyan filayen jiragen sama na kasar.
Sai dai kuma babban bankin bai ce komai ba game da kiraye-kirayen da wadansu masana ke yi cewa a samar da farashin dala na bai-daya, a maimakon halin da ake ciki yanzu inda bankuna ke da farshin da suke sayar wa junansu, CBN ke da farashi a hukumance, sannan kasuwar bayan fage ma ke da nata farashin.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.