Labarai

Calabria: Hotunan gari a Italy da zasu bada N13.6m ga masu son komawa da zama

Wani kauye a kasar Italia ya shirya baiwa duk mai son komawa da zama kudi har N13.6 miliyan Wannan kudin da yankin Calabria zai bada yana yin hakan ne domin habaka yawan masu zama ciki Baya ga wannan makuden kudin da za a baiwa mai son zama, akwai yuwuwar a bada jari domin fara kasuwanci Yankin Calabria na kasar Italiya ya shirya baiwa duk wanda zai tattara komatsansa ya koma garin da zama kudi har N13.6 miliyan, CNN ta ruwaito.

Za a bada wannan kudin ne na tsawon shekaru uku kuma ana son hakan ta janyo hankalin jama’a wurin komawa garin gaba daya.

Calabria: Hotunan gari a Italy da zasu bada N13.6m ga masu son komawa da zama. Hoto daga @explorecalabria Source: Instagram

Ana wannan kokarin ne domin shawo kan matsalar rashin mutane da kauyen ke fuskanta na tsawon shekaru kuma a habaka yawan kauyen mai mazauna 2,000.

Garin yana maraba da mutane masu shekaru ba sama da arba’in ba da haihuwa a duniya.

Sharudan da za a cike kafin a samu N13.6 miliyan

Baya ga cike sharadin dole na komawa garin cikin kwanaki casa’in da nema, dole ne wanda zai zauna ya shirya kafa kasuwanci ko kuma cigaba da wani kasuwanci na garin.

Wani shugaba a yankin mai suna Gianluca Gallo yayin tattaunawa da CNN ya ce akwai yuwuwar a kaddamar da wani tallafi domin kafa cibiyar kasuwanci.

Ya ce: “Muna ta shirye-shirye, watannin tare da lokacin da za a dauka ko kuma za a hada da kauyuka masu mazauna 3,000.

A halin yanzu kauyuka masu yawa sun nuna bukatar jama’a kuma muna fatan idan wannan ya fara aiki, sauran zasu biyo baya.”

Luxury Launches ta bayyana biranen da suka shiga tsarin neman jama’a da: Aieta, Albidonia, Bova, Caccuri, Civita, Samo and Precacore, Sant’Agata del Bianco, San Donato di Ninea da Santa Severina.

#lagithausa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: