Labarai

An cafke wanda ya kashe yar uwarsa ya cire sassan jikinta don yin tsafi

Yan sanda a Jihar Ribas sun cafke wani matashi wanda ya kashe wata yarinya mai shekaru takwas wanda yar uwarsa ce bayan ya yi mata fyade a jihar Ribas.

Ana zargin Ifeanyi Dike dan shekaru 23 wanda yake mataki na Uku a jami’ar jihar Ribas da sace Chikamso Victory a ranar Juma’a da ta gabata.

Kakakin ‘Yan sanda Omoni Nnamdi ya ce wanda ake zargin yayi mata fyade ne daga nan kuma ya kashe ta, ya yanke mata al’aurarta, idanu, harshe, nonuwa ya saka a cikin jakar leda.

An bayyana cewa jami’an tsaro na sa kai ne su ka cafke shi yayin da su ka yi masa zargin alamomi na rashin gaskiya.

“Nan da nan ya jefar da jakar leda, ya karta a guje, su kuma su ka bi shi a guje, su ka make shi.

Bayan ya sha tambayoyi ne jami’an ‘yan sanda su ka dauke shi, inda ya nuna musu wurin da ya yi aika-aikar.

Nan ba da dadewa ba za a gurfanar da shi a kotu.

Da mahaifin yarinyar ya zo wajen ganin gawar ‘yar sa ya ce abin ya gigitashi domin yana da zumunta da wannan matashi da ya aikata wannan mummunar aiki.

” Rudin ta yayi, da ya ga sun Kebe sai ya danne ta da karfin tsiya yayi lalata da ita sannan ya cire abubuwan da zai cire a jikinta kafin aka kama shi.” cewar mahaifin yarinyar.

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.