Kannywood

Burina Shine Yin Aure Da Samun Haihuwa, Cewar Fati Muhammad

Sananniyar jarumar Hausa Fim a shekarun baya Fati Muhammad ta bayyana cewar a yanzu ba tada wani buri a rayuwarta wanda ya wuce ta samu miji nagari tayi aure sannan ta samu haihuwa.

Fati Muhammad ta bayyana hakan ne a yayin tattaunawar da Gidan Rediyon BBC Hausa ya yi da ita a makon da ya gabata.

Tsohuwar tauraruwar masana’antar fim ɗin ta bayyana dalilin da yasa aka daina ganin ta cikin Finafinai a yanzu, inda ta bayyana cewar bai yiyuwa mutum ya ci zamanin shi sannan yaci na wasu, ta janye daga harkar fim ne domin bada dama ga wadanda ke tasowa suma su amfana.

Fati Muhammad wadda a yanzu take gudanar da harkokin kasuwanci da kuma Siyasa,ta bayyana sana’ar Fim a matsayin sana’a mai daraja da kima, amma hakan zai kara tabbata ne idan masu gudanar da harkar sun martaba gami da mutunta sana’ar tasu.

Da aka yi mata tambaya dangane da halin da ƙasa ke ciki na taɓarɓarewar tsaro da kuma hanyar da za’a bi warware matsalar, Fati Muhammad tace babbar hanyar da ya kamata gwamnati ta bi wajen shawo kan matsalar tsaro shine Gwamnati ta inganta jami’an tsaron ta da makamai, domin a halin da ake ciki ‘yan ta’adda sun fi jami’an tsaron gwamnati makamai inji ta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: