Kannywood

Burin Ali Nuhu shi ne ɗansa ya gaje shi a Kannywood

Abin da ya sa nake bin ra’ayi ƴaƴana game da rayuwarsu – Ali Nuhu

Fitaccen tauraron fina-finan Hausa da Turanci na Kannywood Ali Nuhu ya ce inda don ta shi ne ya fi so ɗansa ya gaje shi a harkar fim.

To amma kuma a cewarsa ɗan nasa ya fi sha’awar harkar ƙwallon ƙafa wato Football, dalilin da ya sa kenan ya mara masa baya, domin ya cimma burinsa na Duniya.

Ali Nuhu ya ce ”Abin da zamani ya zo da shi yanzu mafi kyau shi ne, idan ka ga ɗanka ko ‘yarka na son wani abu, matuƙar bai saɓa wa Addini ba to kawai ka goyi bayansa, ka ba shi ƙwarin gwiwa wajen cimma burinsa.”

Ya ƙara da cewa kar ka tilasta wa yaro kan dole cewa sai ya yi wani abu da kaima ra’ayinne bawai gada kayi ba.

Ali Nuhu fitaccen jarumin kannywood ne wanda ya jima yana jan Zarensa In da mafi yawan Jaruman Kannywood na yanzu sunyi Zamanin da suna ƙarƙashin sa.

Da yawan wanda suka zauna dashi sukan ce Mutun ne mai bada Yanci ga Rayuwar mutane a duk lokacin da ya fahimci kanada naka ra’ayin na daban.

Ali Nuhu shine Mai lakabin Sarkin Kannywood inda Adam a Zango kuma ke amsa Yarima, In da ace Ahmad Ali Nuhu zai kasance Jarumi to ana Hasashen zaiyi tasiri fiye da Mahaifin sa saboda yadda Ali Nuhu yake bada Gudunmawa ga wasu mutane ma su zama Jarumai a masana’antar ta Kannywood.

Overall, Ali Nuhu wanne fata zaku yiwa ɗan Ali Nuhu a duniyar kwallon kafa da yake da buri ko wanne shawara zaku bada gareshi.