Buratai ya yi magana kan kashe-kashen Zamfara


0 204

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Babban hafsin sojojin Najeriya, Tukur Yusuf Buratai ya yi magana game da kashe-kashen da ke faruwa a jihar Zamfara.

Bayan da aka tambaye shi wasu na ganin sojojin sun gaza bisa la’akari da cewa ana garkuwa da mutane duk da cewa sun ce suna kokari.

Sai ya ce “duk wanda ya ce sojoji ba sa kokari bai san sha’anin tsaro ba.”

Ya kara da cewa shi tsaro ana fara shi ne daga matakin fako – wato daga kan jama’a.

Ya bayyana cewa sojoji na iya bakin kokarinsu domin tabbatar da cewa suna kare rayukan jama’ar kasar.

An kashe akalla mutum 3,500 yayin da wasu 9,000 suka jikkata a tsawon shekara biyar, kamar yadda sakataren gwamnatin jihar Farfesa Abdullahi Muhammad shinkafi ya shaida wa BBC.

Ya ce alkalunma sun nuna cewa kimanin kauyuka 500 ne aka kai wa farmaki, yayin da aka lalata kuma aka bata hekta 13,000 na kasar gona.

Farfesan ya ce sun tantance hakan ne saboda duk lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari gwamnatinsu tana tura tawaga a kai taimako ga iyalan mamata da wadanda suka jikkata da kuma wadanda suka rasa dukiya.

Har ila yau ya ce akwai mutane da dama da rikicin ya raba da muhallansu. Ya kuma ce rikicin ya fi shafar harkar noma.

Ya ce suna ba jami’an tsaro dukkannin goyon bayan da ya dace wajen ganin an kawo karshen kashe-kashen da ke faruwa a jihar.

A karshen makon jiya ne gwamnatin tarayya ta dakatar da aikace-aikacen hakar ma’adanai a jihar.

Ko mene ne dalilin dakatarwar?

'Yan sandan NajeriyaHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionJami’an tsaron ‘yan sanda da na soja da na farin kaya wato DSS da kuma na asiri duka za su yi aiki tare a Zamfara.

Adamu ya ce an yi hakan ne “bisa la’akari da bayanan sirri da aka tattara, inda ta bayyana karara yadda alakar masu fashi da makamai da masu hakar ma’adanai ba bisa doka ba take, inda kowane sashe ke taimaka wa sashe.”

Kafin gwamnati ta dauki wannan matakin, wasu masu lura da al’amura a jihar Zamfara, musamman wasu daga cikin malaman addini, sun yi ta jefa zargi kamar yadda wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan Intanet ya yi nuni da cewa fafutika ce tsakanin mutanen da ke da karfi a cikin al’umma da abokan huldarsu ‘yan kasashen waje.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 607

- Advertisement -

‘Yan kasashen waje wadanda ke kokarin mamaye dimbin dukiyar ma’adanai da ke shimfide Zamfara, al’amarin da ake ganin shi ya haifar ta’addancin kisan gilla.

Akwai dalilin tababa kan hakan. Ganin yadda ta’addancin kisan gillar ya watsu a cikin jihar, tabbas babu wani sashe da aka kyale, har da harkar hakar ma’adanai.

Matsalar kisan gilla a Zamfara ta samo asali ne tsawon shekaru bakwai da suka wuce. Lamarin ya fara ne kan mafi yawan abin da ake gani na satar shanu.

Al’umomin da ke zaune a yankunan sun dauki matakin kafa rundunar tsaro ta kato-da-gora, wadda ta samu nasarar halaka wasu daga cikin barayin shanun, wadanda daga bisani suka kai harin daukar fansa a kan wasu daga cikin al’umomin, musamman yadda suka rika kai wa shugabanin da ‘yan kato da gorar hari.

Wannan al’amari dai daya bayan daya shi ya haifar da wani har zuwa halin da ake cikin a yanzu.

Har zuwa yau, mafi yawan wadanda aka kashe ko aka yi garkuwa da su da wadanda aka yi wa fashi da makami da wadanda aka tarwatsa su a Jihar Zamfara manoma ne, wadanda ba su da wata alaka da harkar hakar ma’adanai.

Wuraren da munin lamarin ya yi kamari, irin kananan hukumomin Shinkafi da Zurmi da ke Arewacin jihar ba sassa ba ne da ake hakar ma’adanai.

Wuraren da a baya-bayan nan ta’addancin ya far musu, wadanda suka hada da Mada a Karamar Hukumar Gusau da wani bangare na Karamar Hukumar Tsafe, sun fi shahara da noma, ba hakar ma’adanai ba.

Sai dai, Sufeto-Janar din ya ambaci “rahotannin asiri” kuma tunda al’umma ba za su iya bin kadin wadannan rahotannin ba, sai a ba shi damar tabbatar da gaskiyar lamarin. Abu mafi a’ala dai shi ne hukumar ‘yan sanda ta yi kokarin tabbatar da hakikanin gaskiyar rahotannin, ta yadda kada a rufta da su cikin rudani.

An bayar da umarnin dakatar da hakar ma’adanai a Jihar Zamfara ne kwana biyu bayan da Mukaddashin Sufeto-Janar din ‘yan sandan ya kaddamar da shirin ‘Operation Puff Adder’ don shawo kan garkuwa da mutane da ta’adancin kisan gilla a wasu jihohi.

Za a aiwatar da shirin ne tare da hadin gwiwar jami’an tsaron soja da na asiri na DSS. ‘Yan sanda sun ce “za a aiwatar da shirin ne ta hanyar jibge jami’an tsaron da ke da horo da kayan aiki, tare da ba su tallafin rayuwa don zaburarwa.

Sannan da cikakken hadin gwiwar mabambantan jami’an tsaron da aka tsara su don kawar wa kasar nan da matsala, musamman a kan manyan titunan Kaduna zuwa Abuja da Kogi da Katsina da Neja da Zamfara, wuraren da ake fama da aikata miyagun laifuka da tafka ta’asa.

Abin lura a nan tun cikin shekarar 2016, rundunar soja ta kaddamar da shirin ‘Operation Harbin Kunama’ don tabbatar da zaman lafiya a Jihar Zamfara.

Wannan shi ne shiri na uku da aka kaddamar makonni biyu da suka wuce.

Kodayake irin wadannan tsare-tsare yunkurinsu tashin farko yana da tasiri, sai dai sukan kasa kai ga gacin kakkabe ta’addancin kisan gilla a jihar daga karshe.

Mu dai yi fatan a wannan karon shirin kakkabe ta’addancin mai lakabin ‘Operation Puff Adder” tare da dakatar da hakar ma’adanan a Jihar Zamfara za su kawo karshen mummunan kisan gilla da ake fama da shi.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.