-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Bukola Saraki Ya Fi Kowa Bayar Da Gudummuwar Kudi Lokacin Yakin Neman Zaben Buhari A 2015 – Doyin Okupe


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Tsohon me taimakawa shugaban kasa shawara akan harkar watsa labarai kuma me baiwa shugaban yakin neman zaben PDP, Sanata Bukola Saraki shawara, Doyin Okupe ya bayyana yadda ministan watsa labarai Lai Muhammad ya ci amanar Saraki.

A jawabin da yayi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito Doyin Okupe ya bayyana cewa kaf cikin wadanda suka bayar da gudummuwar kudi a lokacin yakin neman zaben Buhari a 2015 babu wanda yakai Saraki bayar da kudi masu tsoka, ya bayar da gudummuwa fiye da ta Bola Tinubu da Amaechi.

Ya kara da cewa a wancan lokacin an zauna aka yi alkawarin cewa idan aka kafa gwamnati za’a baiwa Saraki mukamin kakakin majalisar dattijai da kuma damar kawo ministoci biyu.

Bayan kafa gwamnati ne sai shugaba Buhari ya kira Saraki ya gaya mai cewa ba zai samu minista biyu da aka yi masa alkawari ba saidai guda daya, a haka Sarakin ya hakura.

Bayan kwana biyu sai shugaban kasar ya sake kiranshi yace guda dayan ma bazai samu ba yana rokonshi alfarmar ya hakura a baiwa Lai Muhammad Ministan watsa labarai.

Anan Saraki ya cewa shugaba Buhari me zai hana ya roki Tinubu shima ya hakura da minista daya, sai Buharin ya gaya masa cewa, yayi- yayi da Tinubun amma yaki yadda.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 658

- Advertisement -

Nan saraki yace to kafin ya amince zai koma jiharsu inda shi da Lai Muhammad din suka fito, Kwara dan ya tattauna batun da magoya bayan shi.

Doyin ya kara da cewa da kyar jigogin siyasar Kwara suka yadda aka barwa Lai Muhammad matsayin ministan, sun kuma kira shi suka tattauna dashi, Doyin yace Lai Muhammad yayi ta kuka yana birgima a kasa da rantse-rantse da roko.

Jiga-jigan jam’iyyar sun gayawa Lai cewa ba dan shi zasu amince ba dan basu yadda dashi ba, zasu amince ne kawai saboda kimar shugaban kasa, Muhammadu Buhari da suke gani da kuma dan Allah.

Doyin ya kara da cewa, amma gashi wai yau Lai Muhammad ne gaba-gaba wajan ganin an tumbuke Saraki daga mukaminshi.

#Mikiya

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: