Ku kuma sojoji aikinku shine kare iyakokin kasar nan ba shiga harkar zabe ba, cewarsa
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya jawo hankalin jami’an tsaron sojoji da cewa aikinsu shine kare iyakokin kasar nan amma ba shiga harkar zabe ba.
Atiku ya bayyana hakan ne a wajen taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP da ya wakana a babban birnin tarayya Abuja.
Atiku ya mayar da martani ne akan kalaman da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi na cewa duk wanda aka samu da satar akwati a bindige shi, da kuma amincewa da hukumar sojoji ta yi cewa za ta bi umarnin shugaban kasar.
- Advertisement -
Atiku ya ce shi dai burin siyasar shi bai yadda da zubar da jinin kowane dan Nijeriya ba.
Atiku ya bukaci shugaba Buhari da ya janye wancan kalami nashi na cewa a harbe masu satar akwatin zabe shi ma ya fito ya bayyana cewa ba burin shi na siyasa ne amincewa da zubar da jinin ‘yan Nijeriya ba.
Sannan ya bukaci jami’an tsaro da su taimaka wajen kare kundin tsarin kasar nan.