Siyasa

Buhari ya taya sabon gwamnan Bayelsa na APC murna

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ta dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Bayelsa murnar lashe zaben da aka gudanar ranar Asabar dinna.

A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan yada labarai Femi Adesina ya fitar, shugaban ya ce wannan “nasara ce mai kayatarwa.”

A ranar Asabar din da ta gabata ne aka gudanar da zabukan gwamna a Bayelsa da Kogi.

Sannan hukumar zabe mai zaman kanta INEC, ta sanar da cewa David Lyon na APC ne ya lashe zaben Bayelsa, amma ta ayyana cewa zaben Kogi bai kammala ba.

Sannan shugaban ya yabi magoya bayan APC da ‘yan jihar baki daya, ”wadanda suka kada kuri’unsu cikin kwanciyar hankali, duk da ‘yan rikice-rikicen da aka samu a wasu wuraren.”

Sanarwa ta kara da cewa shugaban ya yi Allah-wadai da asarar rayukan da aka samu a Bayelsa a lokacin zaben, ya kuma mika sakon ta’aziyarsa ga iyalan wadanda suka mutun.

“Tashin hankula a lokutan zabe na dakusar da kokarinmu na nuna wa duniya da al’umma mai tsaowa cewa mu mutane ne da ke iya zabar shugabanni cikin lumana,” a cewar Buhari.

Shugaba Buhari ya ce duk da cewa hukomar INEC da hukumimin tsaron kasar sun yi bakin kokarinsu don yin abin da kasa ta tanadar musu, to abin takaiic ne yadda aka dinga samun tashe-tashen hankula a wasu sassan jihar, “wadanda yawanci ‘yan siyasar da idonsu ya rufe da son mulki ne suka dauki nauyin hakan.”

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement