Labarai

Buhari Ya Sa Nijeria Ta Zama Abun Dariya A Duniya – Reno Omokri

Buhari ya sa Najeriya ta zama abun dariya a idanun duniya – Reno Omokri

Tsohon mataimaki na musamman ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa kasar Najeriya ta zama abun dariya a idanun duniya.

Reno wanda ya kasance daya daga cikin manyan ‘yan adawar gwamnatin shugaban kasa Buhari yayi wannan jawabi ne a yayin da yake bayyana ra’ayinsa game da tambayar kafar yada labarai ta CNN a wani shirin ta na kacici-kacici, inda ta yi tambaya kamar haka : “Shugaban wacce kasa ce bai taka kafar sa a kasarsa ba a tsawon watanni 2?”

 

Inda aka saka kasar Najeriya daga ciki jerin kasashen da aka ambata, wadanda suka hada da kasashen Saudi Arabi da kuma Syria.

Omokri, wanda yayi wannan bayanin ne a shafin sa na twitter,inda wallafa cewa:“Ku kalli yadda shugaba Buhari ya sa aka mai da Najeriya ta zama abun dariya a fuskar Duniya a @CNN!
Ku kalli irin tambayar da ake yi a gasa!”

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana shugaban kasa Buhari a matsayin munafiki.
Yace“Idan ba ku yadda Shugaba Buhari(PMB) munafuki ba ne, ku nemi kanun labarin.

A yanzu Najeriya za a gane cewa canji ba ko da yasuhe ta ke kawo ci gaba ba,” inji shi.