Buhari ya rattaba hannu kan yarjejeniyar yan takaran shugaban kasa
Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannunsa kan takardan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin yan takaran kujeran shugaban kasa a zaben 2019.
An kaddamar da wannan taro ne misalin karfe 3 na rana a farfajiyar taron International Conference Centre da ke birnin tarayya Abuja.