Labarai

Buhari Ya Kira Ni a Waya – Femi Adesina

Mai baiwa shugaban kasa shawara akan harkokin yada labarai Femi Adesina ya bayyana cewa ya samu kira daga shugaban kasa Buhari a jiya Asabar.
Adesina ya bayyana a shafin sa na Facebook cewa wannan abu ya yi matukar yi masa dadi domin kuwa ya dade bai yi magana da shugaban baki da baki ba.
Ya ce Buhari ya kira shi da misalin karfe 2:43 na rana, ya kuma jinjina masa game da yadda yake kokarin kare martabar gwamnatin sa.
Ya ce shugaban ya kuma sanar da shi cewar har yanzu yana kan hutun sa a birnin London na Birtaniya, inda ya fada masa cewar yana fatan zai kara kiran sa a wani lokaci na gaba.
A gefe guda kuma, daya mai taimakwa shugaban akan harkokin yada labarai, Garba Shehu shi ma ya ce ya samu kira daga wajen shugaban, sai dai bai samu damar amsawa ba amma shugaban ya aike masa da sakon Text.
Rahotanni na nuna cewa, shugaban ya kuma kira ministan yada labarai Lai Muhammad a jiya Asabar din, domin ya ware ranar ne ga mataimakan sa akan harkokin yada labarai.
Shugaba Buhari dai na ci gaba da hutawa a birnin London, yayin da mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo ke jan ragamar shugabancin kasar