Labarai

Buhari Ya Kaddamar Da Aikin Shimfida Titin Jirgin Kasa Daga Kano Zuwa Maradi

Daga Comr Abba Sani Pantami

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya kaddamar da titin jirgin ƙasa da zai taso daga Kano ya ratsa Katsina da Jibiya ya tsaya a Maradi cikin jamhuriyar Nijar.

A bikin kaddamar da aikin titin, wanda shugaban ya halarta ta intanet, ya ce titin zai bi ta manyan cibiyoyin kasuwanci kamar Kazaure da Daura da Katsina da Maraɗi.

Haka kuma ya ce hakan zai inganta hanyoyin samun kudin shiga ga kasashen biyu.

Kamfanin Messrs Mota-Engil Nigeria Limited ne ke aikin shimfida titin, kuma zai gina wata makarantar koyon kimiyyar sufuri da titin jirgin kasa.

Shugaba Buhari ya yi kira ga masu zuba jari su sa hannu don ganin an samu ci gaba a fannin tattalin Arziki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: