Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jajantawa iyalan wadanda suka rasu ransu sakamakon wata rumfa da ta fado a kan magoya bayansa a lokacin yakin neman zabe a Maiduguri.
Hakazalika, shugaban ya yi addu’a ga wadanda suka samu raunuka da Allah ya ba su lafiya.
Wasu rahotanni dai sun ce mutum guda ne ya mutu, kusan 40 kuma suka ji raunuka.
Rumfar ta fado ne a daidai lokacin da magoya bayan shugaban suka rinka hawa bisa rumfunan filin wasan domin hangen masu bayani a lokacin yakin neman zaben.
Hakan ne yasa daya daga cikin rumfar ta rikito kan wasu daga cikin magoya bayan shugaban wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa rayuka da samun raunuka.
Shugaban ya bayyana cewa “Na girgiza kwarai sakamakon rasa rayukan da aka samu a filin wasa a Maiduguri. Allah ya jikan wadanda suka rasu ya ba wadanda suka jikkata lafiya.”
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar Borno da kuma hukumar bayar da agaji ta Red Cross da sauran kungiyoyin bayar da agaji suna iya bakin kokarinsu domin tallafawa wadanda abin ya shafa.