Labarai

Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa

Bayan kwashe dogon lokaci bai samu halarta ba wanda hakan ya jawo cece kuce, a yau Laraba dai shugaban kasar ya jagoranci zaman majalisar zartarwa /majalisar ministoci a fadarsa ta Aso villa.

 

Wannan dai shine ya kawo karshen cece kuce da wasu keyi cewa shugaban bai gama samun lafiya ba shi yasa baya iya halartar taron na mako mako.