Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da wasu gwamnonin kasar a birnin Landan na kasar Birtaniya.
Shugaban wanda yake ci gaba da jinya ya gana ne da gwamnonin jam’iyyar APC da yammacin ranar Lahadi, kamar yadda fadar shugaban kasar ta bayyana.
Tawagar da ta kai masa ziyara ta kunshi gwamnonin jihohin Kaduna da Nasarawa da Imo da Ministan Sufuri Mista Rotimi Amaechi da kuma Shugaban Jam’iyyar APC John Oyegun.
Fadar shugaban kasar ta ambato Gwaman jihar Imo Rochas Okorocha yana cewa “shugaban ya samu sauki kuma yana da halinsa na raha.”
Sai dai fadar ba ta bayyana lokacin da shugaban zai koma gida Najeriya ba, amma ta ce dai ya kusa komawa.
Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017
19 ga watan Jan – Ya tafi Birtaniya domin “hutun jinya”
5 ga watan Fabrairu – ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya
10 ga watan Maris – Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba
26 ga watan Afrilu – Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma “yana aiki daga gida”
28 ga watan Afrilu – Bai halarci Sallar Juma’a ba
3 ga watan Mayu – Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku
5 ga watan Mayu – Ya halarci sallar Juma’a a karon farko cikin mako biyu
7 ga watan Mayu – Ya koma Birtaniya domin jinya
25 ga watan Yuni – Ya aikowa ‘yan Najeriya sakon murya
11 ga watan Yuli – Osinbajo ya gana da shi a London
Add Comment