Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya kai ma shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara a Abuja House, dake Landan, jaridar Nigerian Tribune ta rahoto.
Tsohon shugaban kasar ya samu rakiyar wani tsohon gwamnan jihar Osun, Prince Olagunsoye Oyinlola.
An tattaro cewa tsohon shugaban kasar ya isa Abuja House a ranar Asabar, da misalign karfe 9:00 na dare da amincewar Buhari. Wata majiya ta kusa da Obasanjo da Buhari sun bayyana cewa shugabannin sun yi wasu yan muhawara tunma kafin su shiga gidan, inda Obasanjo ya fada ma Buhari cewa ya ji dadin ganinsa cikin koshin lafiya.
Buhari wanda ya nuna farin ciki gaa wannan ziyara, ya fada ma Oyinlola cewa: “Ya mai girma, kayi kyau sosai ïnda Obasanjo da Oyinlola suka maida masa martini da cewa sun ji dadi ganin cewa Buhari ya yi lafiya sosai. Bayan gaishe-gaishe, Buhari da Obasanjo suka shiga wani daki a gidan inda suka gana na tsawon mintuna 40,” cewar majiyar.
Koda dai a lokacin wannan rahoto baá bayyana cikakken bayanin tattaunawar nasu ba, amma dai majiyar ta bayyana cewa ganawar na da alaka da ci gaban kasar. An rahoto cewa shugabannin sun fito daga ganawar da yan mintuna kafin karfe 10:00, wanda daga bisani shugaba Buhari ya take ma tsohon shugaban da Oyinlola baya.
Souce In Naij
Add Comment