Buhari Ya ce ‘Yan Najeriya Su Yi koyi Da Jonathan

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Talla

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan kasar su yi koyi da halaye irin na tsaohon shugaban kasar Goodluck Jonathan.

“Shugaba Buhari ya yi amannar cewa irin rayuwar da tsohon shugaban ya gudanar abar koyi ce ga dukkan matasan kasar,” in ji sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar Mr Femi Adesina ya fitar.

Talla

Ya fitar da sanarwar ce domin taya tsohon shugaban murnar cika shekara 61 a duniya.

Shugaba Buhari ya kara da cewa rayuwar Goodluck Jonathan ta zama izina ga “dukkan mutumin da ke son ya yi koyi, ya yi aiki tukuru sannan ya sanya hannu wajen gina kasa ta gari.”

Ya taya tsohon shugaban kasar murna game da kaddamar da littafin da ya rubuta kan yadda ya tafiyar da mulkin Najeriya.

Talla

Ranar Talata tsohon shugaban kasar ke kaddamar da littafin mai suna, My Transition Hours, don haka ne Shugaba Buhari ya yi kira ga ‘yan kasar su koyi da Mr Jonathan wajen rubuta irin gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban Najeriya.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

Shugaba Buhari da tsohon shugaban kasar cif Olusegun Obasanjo na cikin mutanen da Mr Jonathan ya gayyata wurin kaddamar da littafin.

Goodluck Jonathan dai ya mika mulki a hannu Shugaba Buhari bayan ya kayar da shi a zaben shugaban kasa na 2015, abin da bai taba faruwa ba a tarihin kasar.

Amincewa da shan kayen da Mr Jonathan ya yi ya sa manyan kasashen duniya, ciki har da Amurka sun yaba masa.

Shi kansa Shugaba Buhari ya sha yaba wa tsohon Shugaba Goodluck Jonathan kan arda da shan kayen da ya yi da kuma mika masa mulki ba tare da zubar da jini ba.

Sai dai Shugaba Buhari bai fasa caccakar tsoffin shugaban kasar ba, ciki har da Mr Jonathan, kan abin da ya kira “lalata kasar da kuma rashin aiwatar da ayyukan da suka dace duk da dumbun kudin da suka samu lokacin da suke kan mulki.”

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: