-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Buhari Ya Cancanci Yabo –Dan Sule Lamido


1

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Dan takarar Sanatan Jigawa ta Tsakiya a karkashin jam’iyyar PDP, Mustafa Sule Lamido, ya bayyana cewa ya samu karin karfin guiwar fitowa takara ne dalilin shigo da dokar da ta karfafa wa matasa fitowa takara da Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa.

Mustafa wanda da ne ga tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma tsohon dan takarar shugabancin kasa a karkashin PDP Alh. Sule Lamido, ya yi wannan bayani jiya Alhamis a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.

Ya ce “shigo da dokar ya yi fa’ida domin da a ce ba a shigo da dokar ba, to da bai samu kwarin guiwar fitowa takarar ta sanata ba.”

Mustafa Ya jinjina wa shugaban kasa Muhammadu Buhari da Majalisar Tarayya saboda shigo da dokar da kuma goya mata baya da suka yi.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 653

- Advertisement -

Mustafa ya ce ya na da yakinin samun nasara, saboda abin da ya kira rashin kyakkyawan wakilci da sanatan APC da ke kai, Sabo Nakudu ke yi wa shiyyar mazabar sa.

Mahaifin sa Sule ne jigon siyasar PDP a Jigawa, kuma ya na goya wa Atiku Abubakar baya domin ganin cewa PDP ta yi nasara a Jigawa da kasa baki daya.

#Rariya

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: