Labarai

Buhari Ya Cancanci Dogon Hutu – Ganduje

Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana wa manema labarai jiya a Kano cewa rashin lafiyar shugaba Muhammadu Buhari ba wani abu da ya kamata a yi amfani da shi wajen yada farfaganda ba.
Ganduje ya ci gaba da cewa “Buhari ya cancanci ya samu wadataccen hutu bayan aikin hidimtawa kasa da ya yi, a saboda haka rashin lafiyarsa ko fita hutunsa bai kamata ya zama wani abin muhawara a kai ba”
“Muna fata shugaba Muhammadu Buhari ya kammala hutunsa lafiya ya kuma dawo mana lafiya”
“Duk da kasancewar Nijar kasa mai addinai da al’adu da kabilu mabambanta, bai kamata a ce komai ne za a siyasantar ba. Ya kamata mu fahimci cewa kowane mutum zai iya samun rshin lafiya. Kuma da wasu ke tambaya ko mun kira shi, ya kamata su san cewa shugaba Buhari hutu ya tafi don yana bukatar hutun. In har yana hutun kuma sai ya yi magana da kowane gwamna, to, ina amfanin hutun da ya tafi kenan?”
“Mutane na amfani da kowace dama su yi ta maganganu maras kan gado. Alhali kafin shugaba Muhammadu Buhari ya bar kasar nan sai da ya rubutawa majalisa cewa zai je hutu kuma za a duba lafiyarsa. Ai ya kamata a ce wannan bayani da ya yi ya wadatar”