Buhari ya buƙaci hafsoshin soja su dawo da tsaro kafin damuna

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya faɗa wa sabbin hafsoshin tsaron ƙasar cewa su tabbata sun sauke nauyin da ke kansu na dawo da zaman lafiya “kafin zuwan damuna”.

Buhari wanda ya bayyana haka a yau Juma’a yayin bikin bai wa shugabannin tsaron muƙamansu a fadar Aso Villa, ya umarce su da su “ceto Najeriya daga matsalar tsaro cikin gaggawa.”

Ya ce: “Yayin taronmu kan tsaro na awa huɗu da muka yi ranar Talata, na ɗaura muku alhaki a matsayina na Shuhgaban Tsaro da ku fita filin daga domin ku kare wannan ƙasa.

“Yan makonni kaɗai gare ku don ku yi hakan saboda damuna. Muna sa ran ‘yan ƙasa su samu ƙwarin gwiwar komawa gonakinsu saboda kar mu sake shiga matsala ta barin filin daga kuma mu kasa samar da isasshen abinci ga ƙasa.”

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 731

Najeriya na fama da matsalolin rashin tsaro a kowane ɓangare na ƙasar, musamman a arewa maso gabas, inda Boko Haram ke ci gaba da kai hare-hare, da kuma arewa maso yamma, inda ‘yan fashi ke kashe mutane a kullum.

A ƙarsen watan Janairu ne Buhari ya sauya hafsoshin tsaron ƙasar tare da maye gurbinsu da sabbi.

Sabbin hafsoshin tsaron su ne:

  • Janar Leo Irabor – shi ne aka naɗa babban hafsan tsaro
  • Janar I. Attahiru – babban hafsan sojan ƙasa
  • Rear Admiral A.Z Gambo – babban hafsan sojan ruwa
  • Air-Vice Marshal I.O Amao – babban hafsan sojan sama
Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: