Tsofaffin shugabannin jam’iyar PDP na kasa wato tsohon gwamnan Jihar Bauchi Alhaji Ahmed Adamu Mu’azu da Bamanga Tukur sun sauya sheka zuwa Jam’iyar APC a yau, a yayin gudanar da yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyar APC a garin Bauchi.
Haka kuma a tare da tsohon shugaban jam’iyar ta PDP za a karbi wasu manyan jiga-jigan jam’iyar ta PDP da suka sauya sheka zuwa jam’iyar ta APC daga jihar ta Bauchi wadanda suka hada da:
Alhaji Babayo Garba Ganawa
(Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyar PDP ta Kasa na yankin Arewa), Alhaji Yayale Ahmed wanda ya rike mukamin Sakataren Gwamnatin Tarayya a lokacin PDP da kuma Alhaji Kaulaha Aliyu.
Haka kuma a Jihar Sokoto ma jam’iyar ta APC ta yi babban kamu duk a cikin wannan satin inda mai bada shawara akan harkokin Shari’a na jam’iyyar PDP a Jihar Sokoto wato Alhaji Nasiru Sahabi Tambuwal shi ma ya fice daga jam’iyar ta PDP zuwa APC.
- Advertisement -
Haka ma a Jihar Kebbi, Sakataren Jam’iyar ta PDP shima ya fice daga jam’iyar zuwa jam’iyar APC
Hakama a Jihar Kaduna, tsohon shugaban Majalisar dokoki ta jahar Kaduna wato Bashir Zubairu Usman shi ma ya fice daga jam’iyar ta PDP zuwa Jam’iyar APC .
A Jihar Gombe an samu dan takarar kujerar gwamna Alhaji Abdulkadir Hamma Sale ya bar jami’yar ta PDP zuwa jami’yar APC da kuma UD Kedengs Jarman Tangale shi ma ya koma jami’yar APC da kuma babban kamu da jami’yar APC na Kodinetan yakin neman zaben Atiku Abubakar na shiyar Arewa maso gabas Sanata Sa’idu Umar Kumo duk a jihar Gombe.
Sai gashi shima mataimakin shugaban Majalisar Dattawa Ike Ekwurenmadu an jiyo shi yana cewa dole ya goyi bayan shugaba Muhammadu Buhari saboda irin ayyukan alherin da ya gudanar a yankin Kudu Maso gabas inda Sanatan ya fito.