-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Buhari Na Jiran Tabbatar Ma Sa Da Nasararsa


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Shugaban Najeriya mai ci Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC na jiran tabbatar da nasarar sake lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar Asabar.

Sakamakon jahohi 36 da aka bayyana ya nuna Buhari ya ba babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ratar kuri’a sama da miliyan hudu.

Zuwa yanzu Atiku yana da yawan kuri’a 11,262,978, bayan kammala tattara sakamakon dukkanin jihohin Najeriya.

Tuni dai jam’iyyar PDP ta yi watsi da sakamakon, wanda ta kira aringizon kuri’u saboda ya saba wa sakamakon da tattara daga wakilanta.

Sai dai jam’iyyar APC mai mulki ta yi Allah-wadai da matakin da PDPn ta dauka.

A shekarar 2015 aka fara zabar Shugaba Buhari bayan da ya kayar da shugaba mai ci a lokacin, Goodluck Jonathan, na PDP.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 86

- Advertisement -

Jam’iyyar ta PDP ta shafe shekara 16 tana da mulkar Najeriya.

Kuma Buhari ne ya zamo dan siyasar adawa na farko da ya lashe zabe a kasar.

Dan takarar da ya fi samun kuri’u ake ayyanawa a wanda ya yi nasara a zagayen farko, in dai har ya samu kashi 25 cikin 100 na kuri’un da aka kada a kashi biyu cikin uku na jihohin kasar.

‘Yan takarar shugaban kasa 73 ne suka yi rijista, amma an fi yin gwagwarmaya ne tsakanin Buhari da Atiku.

Dukkansu sun fito ne daga arewacin kasar inda Musulmai suka fi yawa, kuma dukkansu sun haura shekara 70, yayin da mafi yawan ‘yan kasar da suka yi rijistar zabe ‘yan kasa da shekara 35 ne.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: