Yan takaran kujeran shugaban kasan Najeriya karkashin jam’iyyar Peolples Demcratic Party PDP, da na jam’iyyar All Progressives Congress APC, Atiku Abubakar da shugaba Muhammadu Buhari sun isa dakin taron International Conference Center ICC dake birnin tarayya Abuja.
Manyan yan siyasan biyu sun hadu a lokaci daya karo na farko tun lokacin da suka fara yakin neman zabe ne domin rattaba hannu kan takardan lumana gabanin zaben ranan Asabar.
Bayan isowar yan takaran, Janar Abubakar ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a wannan zaben da su tabbatar da zaman lafiya kafin zabe da bayan zabe.
Ya yi kira da yan takara suyi amfani da kwanaki da suka rage domin magana da jama’a da magoya bayansu sabanin soke-soken juna. Ya yi bayanin cewa yana jaddada haka ne saboda a daina bukatar gayyatan yan kasashen waje a zaben gaba.
Atiku Abubakar ya zo tare da shugaban jam’iyyar PDP, Uche Secondus, shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da wasu jiga-jigan jam’iyyar.
Hakazalika shugaba Buhari ya isa taron tare da shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshiomole, tare da wasu manyan jami’an gwamnati.