Labarai

Buhari ba zai yi murabus ba -martanin APC ga masu kiran shugaban yayi murabus

Buhari ba zai yi murabus ba -martanin APC ga masu kiran shugaban yayi murabus

tace ko a America anyi shugaban kasar da ya mulki kasar a halin jinya.

Reshen matasa na jam’iyyar APC ta gargadi fitaccen dan wasan Baburan nan, Charlyboy da duk wasu gungun mutane dake kiran shugaban kasa Buhari yayi murabus da su daina domin shugaban ba zai sauka ba.

PoliticsNGR ta wallafa sanarwar a shafinta, sanarwar dauke da sanya hannun shugaban matasan, Collins Edwin, yace shugaba Buhari yana samun sauki kuma suna da yakinin zai koma ofis dinsa.

 

Sanarwar tace ko a America anyi shugaban kasar da ya tafiyar da kasar a cikin matsanancin rashin lafiya na mutuwar sassan jiki.

Hausa times ta ruwaito a shekarar 1919, shugaba Woodrow Wilson na Amurka ya fada matsananciyar jinya amma Amerikawa basu siyasantar da rashin lafiyarsa ba kuma bai yi murabus ba a haka ya tafiyar da mulkin kasar saboda haka ba Nigeria ce farau ba.

Ballantana ma mista Buhari zai dawo da zaran likitocinsa sun sallameshi inji sanarwar

ME ZAKU CE ?

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Advertisement