-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Buhari Ba Ya Karya –Ministar kudi


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ministar kudi Zainab Ahmed ta kare shugaban kasa Muhammadu Buhari kan ayyukan da ya ce gwamnatinsa na aiwatarwa sa’ilin gabatar da kasafin kudin na 2019, a zauren majalisar dokokin kasar.

Ministar kudin ta ce babu yadda za a yi shugaban kasar ya fadi abinda ba gaskiya ba ne.

A cewar ta “Shugaban kasa mutum ne mai gaskiya kuma tsayayye, ba yanda za a yi ya ce an yi abu wanda ba a yi ba.”

A cikin hirar da ta yi da BBC, ta ce dukkanin ayyukan da shugaban kasar ya fada suna cikin kasafin kudin shekarar 2018, wanda zai tsaya a watan Yunin shekarar 2019.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 653

- Advertisement -

Ta kuma ce an sake sanya ayyukan cikin kasafin kudin shekarar 2019, domin tabbatar da cewa an kammala su.

An dai samu rudani a lokacin da shugaban ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2019 a zauren majalisar dokokin ta Najeriya.

Inda wasu wakilan majalisar suka rinka katsalandan a lokacin da shugaban kasar ke jawabi, musamman a lokacin da yake bayani kan nasarorin gwamnatinsa.

Sun rinka cewa ‘karya’, ko ‘a ina?’, wasu kuma na cewa ‘ba haka ba ne.’

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: