Wani mai taimakawa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce shugaban kasar ba ya boye-boye kan rashin lafiyarsa.
Mallam Bashir Ahmad, mai bai taimakawa shugaban na Najeriya kan shafukan sada zumunta, ya shaida wa BBC cewa fitowar da ake yi ana sanar da ‘yan kasar a duk lokacin da shugaban zai tafi kasar waje domin yin jinya alama ce da ke nuna cewa ba shi da abin boyewa.
A cewarsa, “Rashin lafiyar Shugaba Buhari ba a boye take ba domin dukkan tafiye-tafiyen da ya yi domin yin jinya babu wadda bai gaya wa ‘yan Najeriya cewa zai tafi ba. Ya yi tafiya sau hudu zuwa biyar kuma babu wacce bai fada wa ‘yan kasar cewa zai je a duba lafiyarsa ba.
“Tafiya ta baya bayan na ita ce wacce ya ce zai kwana goma, kuma da aka ga ba zai dawo ba saboda likitoci ba su amince ba, sai da aka fada wa majalisun dokoki.”
Kakakin na shugaban Najeriya ya ce fadar shugaban kasar ba ta fadi lalurar da Shugaba Buhari ke fama da ita ba ne saboda abu ne da ya shafi mutum da likitansa.

“Kowa yana kwanciya rashin lafiya kuma hakan tsakaninsa ne da likitansa, don haka abin da ya fi muhimmanci shi ne shugaban ya mika ragamar tafiyar da kasar ga mataimakinsa wanda zai ci gaba da gudanar da ayyukan ci gaban kasa,” in ji Mallam Bashir Ahmad.
Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017
19 ga watan Jan – Ya tafi Birtaniya domin “hutun jinya”
5 ga watan Fabrairu – ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya
10 ga watan Maris – Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba
26 ga watan Afrilu – Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma “yana aiki daga gida”
28 ga watan Afrilu – Bai halarci Sallar Juma’a ba
3 ga watan Mayu – Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku
5 ga watan Mayu – Ya halarci sallar Juma’a a karon farko cikin mako biyu
7 ga watan Mayu – Ya koma Birtaniya domin jinya
25 ga watan Yuni – Ya aikowa ‘yan Najeriya sakon murya
11 ga watan Yuli – Osinbajo ya gana da shi a London
23 ga watan Yuli – Wasu gwamnoni da shugaban jam’iyyar APC sun ziyace shi a London
Add Comment