-Advertisement-Home | Wakokin Hausa | Wakokin Hip Hop | Bidiyos | Kannywood News | Labarai | Dadin Kowa | English News
Advertise With Us | Upload Ur Music
Email:- Send Email

Budaddiyar Wasika Zuwa Ga General Tukur Buratai Da Sauran `Yan Najeriya


0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Budaddiyar Wasika Zuwa Ga General Tukur Buratai Da Sauran ‘Yan Najeriya

Sheriff Almuhajir PhD
Yobe State University, Damaturu.
24th-11-2018

Ban so in ce komai ba bayan adduah ga sojan Najeriya da ya sadaukar da rayuwar shi akan kasar mu ba, musamman akan al-ummar mu ta Borno da Yobe ba.

Amma saboda yadda naga yan kasa sun shiga rudani nayi niyyar fidda rubutu a matsayin matashiya ga yan kasa akan halin da ake ciki.

Amma kafinnan, ina son kowa ya fahimta cewa tsawon shekaru goma kenan cif Najeriya na cikin halin yaki, cikin shekarun nan goma 6 na farko an ragargaji kowa a kasar nan, tun ana kashe soja, yan sanda, civil defence, road safety, har aka dawo kashe al-ummar gari, tun daga Maiduguri har Abuja da Kaduna. Kano sai da ta zama sansanin BH.

Ko har mun mance da harin da aka kaiwa Sarki Ado, harin Kristoci a old site BUK, da uwa Uba masallacin Sarki?

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 14

- Advertisement -

Bamu yi tsammani za’a samu sassauci cikin lokaci kankani kamar haka ba, yan sanda, civil defence, road safety su dawo sanya uniform, mutanen Kano, Kaduna, Abuja, Suleja su mance da hare-haren BH, A nemi Shekau a rasa, sojan Najeriya ya dawo yana kai farmaki maimakon gudun da ya saba a baya. Mun komo rayuwar mu kamar ta baya, babu check points babu night search, Alhamdulilah.

Duk da mun san cewa da zuwan Buharine wadannan abubuwa suka samu cikin ikon Allah, wasun mu sun mance cewa yaki ake yi, shi kuma yaki yau nasara gare ka gobe ga abokin gabar ka.

Bayan wannan musibah da ta faru jiya, Sai wasu ke rubuce-rubucen nuna kosawa da gajiyawa, maimakon suyi rubuce-rubucen karawa sojan Najeriya kaimi da karsashin fuskantar makiyan shi.

Wannan kuma kuskure ne babba.

Wasun mu kuma na kira cewa ayi sulhu da BH, sun mance ne cewa Boko Haram babu sulhu da zaka yi da su bar kashe mutane, saboda su iya fahimtar su sai sun kashe mutanene su zasu shiga tasu aljannar, to tayaya zasu saki aljannar su saboda wani sulhun duniya? Tun zamanin Jonathan gomnatin Najeriya ke neman hanyar sulhu da su, su kuma sukayi amfani da wannan d

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: