BUDADDIYAR WASIKA GA GWAMNA KAN DALIBAN KANO DAKE KARATU A SUDAN-NASIRU SALISU ZANGO

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

BUDADDIYAR WASIKA Ga BABA NA GWAMANAN KANO….

Ina yiwa mai girma Gwamna Dr Ganduje barka da juma’a…

Wasu Abubuwan Masu Alaka
Talla

[Music] Saddam Ungogo -Yar Kanon Dabo

1 of 32

Ya mai girma gwamna Khadimul Islam,ina fatan wannan juma’ar ta riske ka lafiya tare da iyalan Ka. Ina jinjina maka a matsayin Ka Na wanda ke haba haba da iyalai wajen kyautata musu da kokarin sun yi rayuwa ingantacciya, hakika duk wanda ya yi sa’ar uba ya yi sa’a, kuma ina zaton Essalansy baya nuna bambamci a tsakanin yayan sa domin yin haka malamai sunce lagahu ne. Mai girma gwamna bahaushe fa yace duk abin da lauje ya dauko ciyawa ce, dan haka a matsayin Ka Na gwamnan mu na Kano, kuma dattijo da Allah ya lamuncewa Ka zarta shekaru 70 nasan tabbas Ka cika ka’ida ta zama uban mu maganin kukan mu. Dan haka nake kyautata zaton bazaka nuna bambamci tsakanin mu da sauran wadanda ka haifa ba. Ya mai girma Gwamna wallahi yau Na tashi cikin tashin hankali da bacin rai sai dai kawai na cigaba da ambaton innalillahi wa inna ilayhi rajiuun, na kasa rike kwallar da ta cika ido na har sai da ta fito Ta zama hawaye, domin yan uwa na ‘yayan ka ya gwamna dake kasar Sudan sun aiko min da sabon sakon irin masifar da suke ciki, domin wannan karon sun aiko da muryoyin su sun bayyana yadda suke wulakanta a Sudan. Matan cikin su dake jami’ar Oundurman sun gama karatun amma ba a basu sakamako ba saboda Baban mu gwamna bai biya hakkin makaranta ba, haka kuma me gidan da suke haya ya kwace musu paspo saboda bashin dake kansu Baban mu bai biya ba, ga rashin mutsuguni ga rashin abinci ga kuma fargabar yau da gobe har wasu daga cikin su sun fara kamuwa da cutar damuwa, kamar yadda suka sanar dani. Haka zalika akwai sauran dake jami’ar Elrazi su kuma basu idar da karatun ba amma makaranta ta hana su shiga aji wai saboda Baban mu ya ki biyan kudinsu,haka suma ga matsalar kudin abinci da yau da gobe har sun fara sayar da kayan karatu suna cin abinci.Baba gwamna nasan cewar yar uwar mu Dr Balaraba ma aikin likitanci ta karanta kamar wadannan yan uwa namu, to dan Allah Baba gwamna da ace lokacin karatun ta an mata irin wannan kamshin mutuwa ya Baba zai ji? Dan Allah Baba Ka Kawo karshen matsalar daliban nan koda kuwa aikin gadar Dangi da cigaba da aikin france road zai tsaya, dan Allah Baba Ka biya kudin kannen nan namu koda kuwa zaka rasa abin biyan yan kwangila domin cigaba da karasa aikin yayan ka dake wata duniyar yafi gaggawa kan biyan masu aikin titi. Baba rashin biyan wannan kudi zai sa mu yanke kauna mu fara tunanin ko baka dauke mu yaya ba, domin kuwa bamu ga kana nuna irin wannan hali akan sauran yan uwan mu Na cikin gida ba. A karshe nake shaidawa Baba gwamna cewar idan fa ba a dauki mataki ba, zamu tafi kotu akan hakkin wadannan kanne namu, ko kuma ni Na fito filin cikin yanayin zanga zangar lumana tare da duk wanda yaga dacewar haka muzo bakin gidan mu na gamman hawus muyi zaman dabaro har sai Baba ya amsa kukan yayansa ya kuma tabbatar da adalci a tsakanin mu. A karshe nake jaddada addua ta gare ka gudun kada duniya tace yayan Baba sun yi masa bore akan kudin makaranta. Ina rokon duk wanda ke da iko ya isar da wannan wasika tawa ga Baban mu Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Nasiru Salisu Zango

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: