Kannywood

BUƊAƊƊIYAR WASIKA ZUWA GA SHUGABAN ƘASA MUHAMMADU BUHARI

Watanni huɗu da suka gabata…, har yanzu dai bata sauya zani ba😭😭😭

“BUHARI NE ZAI AMSA!!!

BUƊAƊƊIYAR WASIKA ZUWA GA SHUGABAN ƘASA MUHAMMADU BUHARI

Cikin girmamawa gareka shugabanmu, kaine wanda muka zaɓa babu haufi da kokwanto game da nagartarka fiye da kowane shugaba da muka yi a baya. Mun yi tsayuwar daka wajen yin addu’o’i da neman taimakon Allah dan ganin cewa ka zama shugaba a wannan ƙasa tamu. Tunda ko haka ne, kenan muna da haƙƙi na gaya maka gaskiya a lokacin da muka ga ka saki layin da muka yi zaton kasancewarka a kai.

A zamanin mulkin gwamnatocin da suka gabata, ka shiga jerin waɗanda suka riƙa jagorantar zanga-zangar lumana kan matsalolin da suka addabi jama’a, tare da gayawa kowacce gwamnati gaskiya kan zahirin halin da talakan ƙasata Najeriya ke ciki.

A yanzu ma dai bayan hawa mulkinka da shekaru huɗu zuwa biyar lokacin bai bam-bamta da bayan ba, muddin magana ake yi ta matsala da ƙunchin rayuwa, sai ma ta’azzara da lammura suka ƙara yi.

Ƴancin kasancewarka ɗan ƙasa da damar yin zanga-zanga kan wani abu da ke damunka, bai zama tauyayye ga sauran al’umma dake rayuwa a zamanin mulkinka ba. Muna da haƙƙi mu koka, kuma dole a sauraremu tare da kawo mana mafita kan matsalolin dake damunmu.

Idan har a baya za ka yi kira ga malaman addinai da su yi addu’o’i tare da yin Alƙunuti kan taɓarɓarewar lammuran tsaro, yanzu muma zamu iya yin kira garesu da su yi Alƙunuti ga taka gwamnatin, tunda dai ka iya ɗaukar matakan da zasu cutar da mu a cikin mulki, amma ka kasa ɗaukar matakan da suka dace domin warware matsalolin dake damunmu.

Kullum zubar da jinin bayin Allah ake yi, ana sace na sacewa a kashe na kashewa, a riƙa cinikin mutane kamar dabbobin layya, wasu ma koda sun iya biyan kuɗin fansa kashesu ake yi sai-dai a tsinci gawa, duk da sunan ta’addanci na ayyukan ƴan bindiga-daɗi.

Ta kai gargarar da har cikin gidan bayin Allah ake shiga da bindigogi a ɗauke mutum a yankin nan namu na arewa, har a jiharka ta Katsina irin wannan na faruwa. Kai ta ɓangaren Boko Haram har gwamna Zullum na Borno aka kaiwa farmaki aka kashe jami’an tsaronsa cikin jini. Kuma kai da kanka ka jefa ayar tambaya ga shugabannin hukumomin tsaro a wani zama da kuka yi can baya,

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.