Labarai

Boye bayanai tsakanin hukumomin tsaron Najeriya ne ya sa ba a sami galaba kan Boko Haram ba – Kasar Amurka

Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa cin dunduniyar juna tsakanin hukumomin tsaron Najeriya, ta hanyar boye bayanan tsaro na sirri ba tare da bayyana wa daya bangaren tsaron ba, shi ne makasudin kasa yin galaba a kan Boko Haram.

Wannan bayani ya na kunshe ne a cikin wani rahoto a kan ta’addanci na 2016, mai suna Country Report on Terrorism, wanda hukumomin tsaron Amurka su ka wallafa.

A misali, kamar yadda rahoton ya nuna, matsalar yadda jami’an tsaro na farin kaya, SSS ke yin biris, su na kin bayyana wasu bayanai na sirri ga EFCC, zai yi wuya a iya gano yadda ko wadanda ke da hannu wajen kashe kudade su na taimakon ‘yan ta’adda.

“Yayin da rundunar sojojin Nijeriya ce ke da alhakin dakile ta’addanci a Arewa maso Gabacin kasar, sauran hukumomin tsaron kasar su ne ke aikin hana faruwar ta;addanci, kamar irin su hukumar SSS, rundunar ‘yan sandan Najeirya da kuma Ma’aikatar Shari’a.

Rahoton kuma ya yi tsokaci dangane da yadda hukumar EFCC da Ma’aikatar Shari’a ke nuna kasala da lalaci wajen gurfanarwa da hukunta masu hannu wajen taimaka wa Boko Haram da makudan kudade.

 

Source Premiumtimes Hausa

About the author

Haarun

Co-founder Arewablog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.