Get New DJ Mixes
Labarai

Boko Haram ta saki bidiyon ma'aikatan hako mai

Ranar Talata ne dai Boko Haram din ta yi wa tawagar da mutanen suke kwantan bauna

Kungiyar Boko Haram bangaren Albarnawi ta saki wani bidiyo da ke nuna mutane uku da ta ce ta kama lokacin wani harin sunkuru da ta kai wa ma’aikatan hakar mai a jihar Bornon Najeriya.

Bidiyon wanda gidan talbijin na Channels a Najeriya ya ce an aike masa, ya nuna mutanen uku zaune sannan bayansu akwai wani kyalle.
 
Biyu daga cikin mutanen sun ce ma’aikatan sashen kimiyyar kasa ne na jami’ar Maiduguri, a inda shi kuma na ukun ya ce shi direba ne.
Mutanen dai sun nemi gwamnati da ta kai musu dauki.
A ranar Talata ne dai ake zargin kungiyar Boko Haram ta abka wa wata tawagar ma’aikatan aikin hakar man fetir da ke tafe cikin rakiyar sojoji da ‘yan sintiri.
Kuma yawancin ma’aikatan sun fito daga jami’ar Maidguri ne, duk kuwa da cewa akwai ma’aikatan kamfanin mai na kasar wato NNPC.
Kamfanin na NNPC dai ya ce wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun sace masu binciken mai guda goma da suke masa aiki a jihar Borno.
Sai dai sojojin Najeriya sun ce sun ceto wasu daga cikin mutanen al’amarin da har ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji guda tara.
Rahotanni sun nuna cewa sakamakon kwantan baunar da kungiyar ta kai mutane fiye da 40 ne suka mutu da suka hada da sojoji da ‘yan sintiri.

About the author

Mr. ArewaBlog

C.E.O/Founder ArewaBlog

Add Comment

Click here to post a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.