Labarai

Boko Haram Ta Nada Sabon Shugaba, Bakura Modu, Wanda Zai Maye Gurbin Marigayi Shekau

Daga Abubakar A. Adam Babankyauta
Bakura Modu, shine wanda ya yi jawabin tabbatar da mutuwar Shekau a sabon bidiyon da kungiyar ta fitar yana karfafa ma mabiyansa gwiwa tare da cewa za su dauki fansar kisar Shekau a kan ISWAP.

Sabon shugaban shine Bakura Modu wanda ya yi jawabi a bidiyon da kungiyar ta fitar a baya-bayan nan kamar yadda wata majiya ta tabbatar A cikin bidiyon, Bakura Modu ya karfafawa yan ta,ddan gwiwa tare da jadada cewa za su dauki fansar kisar Shekau a kan ISWAP

Wato jama,a kamar yadda wata majiya ta tabbatar da cewa Kungiyar Boko Haram ta tabbatar da mutuwar shugabanta Abubakar Shekau a cikin wani hoton bidiyo da ta fitar sannan ta nuna sabon shugabanta, Bakura Modu, wanda ya lashi takobin daukar fansar kisan da aka yi tsohon shugabansu Shekau.

VOA ta ruwaito cewa wata majiya da ke kusanci da kungiyar Boko Haram ne ta samarwa kamfanin dillancin labarai na AFP bidiyon, sannan wata majiyar daban ta tabbatar wanda ke jawabin wato Bakura Modu shine sabon shugaban kungiyar.

Bidiyon ya haska Bakura tare da wasu yan ta,addan kungiyar a zagaye da shi a bayansa tamkar dai yadda kungiyar ta saba yi a duk lokutan da za ta fitar da sanarwar makamancin wannan kamar yadda VOA ta ruwaito.

Bakura ya karfafawa yan ta,addan gwiwa yana mai cewa kada su karaya wurin yaki da abokan gaba duba da abin da ya samu Shekau.

Kazalika, ya yi kira a gare su da su yi watsi da shugaban ISWAP, Abu Musa Al-Barnawi, yana mai jadada cewa za su cigaba da yaki da ISWAP har sai sun dauki fansar kisar Shekau da wasu kwamandojinsu da aka kashe.

Muna rokon Allah ya, Assasa wutar rikici tsakanin yan ta,addan boko haram da ISWAP wacce zata zama silar yakin da zasu dinga hallaka kansu da kansu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: