Labarai

Boko Haram sun kar 18, sun kuma wawashe dukiya da sace jama’a a sansanin gudun hijira a Banki

Jajiberin Sallah da tsakar dare suka kai hare-haren

Sun kone tantuna sun sace mata da yara

Babu bindiga ko bam a tare dasu, wukake ne kawai da takubba

A tsakar daren alhamishin nan ne, ‘yan Boko Haramun suka lababa mazaunin ‘yan gudun hijira da ke garin Banki a karamar hukumar Bama ta jihar Borno, suka kuma yi mummunar barna tare da satar yara da abinci.

 

Sun dai iso da misalin sha dayan dare, suka kuma lababa cikin bukkoki da wukake suna kashe mutane, suna kuma yanka su, babu harbi ko bam saboda haka, ba’a ankare da wuri ba.

Sansanin na Banki, na da ‘yan gudun hijira 25,000, kuma yana dab da iyakar kasar nan ne da kasar Kamaru.

Watakil sai jami’an tsaro sun fara rabawa jama’a bindigogi su kare kansu tunda sun gaza, sannan a sami sauki, ko Boko Haram in da ta san inda zata je akwai tirjiya da makamai, zasu fara shakkar talakawa..

 

Souce In Naij