Boko Haram Na Yankin Tafkin Chad Sun Shiga Uku

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Dattawa Dattawa

Rundinar hadin gwiwa na kasashen dake iyaka da yankin tafkin Chadi (Nigeria, Kamaru, Nijer da Chadi) wato Multi National Joint Task Force (MN/JTF) ta kaddamar da zabon salo na yaki da Boko Haram/ISWAP wanda rundinar tayiwa take da OPERATION ‘YANCIN TAFKI

Talla

Wannan mataki da rundinar MNJTF ta dauka ya biyo bayan zafafa hari da ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP suke kaddamarwa a yankin na tabkin Chadi suke addabar mazauna garuruwan da suka hada da Baga, Arege, Metele da sauransu

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 661

Kuma dalilin da yasa rundinar sojin hadin gwiwa na kasashen suka kaddamar da OPERATION ‘YANCIN TAFKI shine domin a kaddamar da harin kare-dangi akan ‘yan Boko Haram din da suke yankin na tafkin Chadi a share ruhinsu daga doron duniya, za’a yakesu da dukkan karfin soji har sai an tabbatar da kawo karshensu a yankin

Wannan sanarwan ya fito ne daga Kanar Timothy Antigha jami’in hulda da jama’a na rundinar MNJTF na Kasar Chadi

Muna rokon Allah Ya kawo mana karshen annobar kungiyar Boko Haram da masu daukar nauyinsu Amin

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: