Wasu ma’aikatan Jami’ar Maiduguri guda biyar sun mutu yayin da sojojin kasar ke kokarin kwato su daga hannun kungiyar Boko Haram, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Shugaban kungiyar malaman jami’o’i a Najeriya (ASUU) reshen Jami’ar Maiduguri, Dokta Dani Mamman, ya ce ma’aikatan jami’ar biyar ne suka rasu cikin ma’aikata tara da suka je aikin binciken danyen mai a yankin Tafkin Chadi.
Tun daga farko dai rundunar sojin Najeriya ta fitar da sanarwar cewa ta ceto wasu daga cikin ma’aikatan da Boko Haram ta kama a lokacin da suka je binciken danayen mai a yankin.
A sanarwar da kakakin rundunar, Sani Usman Kukasheka, ya fitar rundunar sojin Najeriya dai ta ce sojoji tara ne suka rasu a lokacin da suke neman kwato malaman daga hannun kungiyar Boko Haram.
A hirarsa da abokin aikinmu, Aliyu Tanko, Dokta Mamman ya ce mutanen jami’ar na fatan za a samo sauran ma’aikatan jami’ar hudu da rai yayin da yake jajantawa sojin kasar game da rasa dakarunta da ta yi.
Add Comment