Biyo Bayan Kudirin Tsigeshi Kakakin Majalisar Dokokin Kano yayi Murabus

0

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Abdulaziz Garba Gafasa, da kuma wasu shugabannin majalisar biyu sun sauka daga muƙamansu.

Gafasa ya bayyana sauka daga muƙamin nasa ne cikin wata wasiƙa da ya aike wa akawun majalisar mai ɗauke da kwanan watan 14 ga Disamba.

“Ni Abdulaziz Garba Gafasa, ina sanar da kai tare da sauran jama’a cewa na sauka daga muƙamina daga ranar da aka rubuta a sama bisa dalilai na ƙashin kaina,” wani ɓangare na wasiƙar ya bayyana.

Sai dai wata majiya ta faɗa wa BBC cewa kakakin ya sauka ne yayin da ‘yan majalisar ke yunƙurin tsige shi daga muƙaminsa.

A jiya Litinin ne ‘yan majalisar suka taru a otel ɗin Bristol Palace da ke birnin na Kano domin tsige shugaban nasu, sai dai Abdulaziz Gafasa ya je wurin domin shawo kan lamarin amma ya gaza samun nasara.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 736

‘Yan majalisar sun bayyana cewa rashin biyan buƙatunsu ta hanyar kare muradun gwamnatin jihar na daga cikin dalilan da ya sa suka sauke shi daga muƙaminsa.

Kazalika sun zarge shi da nuna wariya ga wasu daga cikinsu, ciki har da ‘yan jam’iyyarsa ta APC.

Anjima a yau ne ake sa ran za a zaɓi sabon kakakin majalisar kuma Honarabul Hamisu Ibrahim Cidari ne ake sa ran za a zaɓa, wanda da ma shi ne mataimakin Abdulaziz Gafasa.

Rikici ya kunno kai ne a Majalisar ta Jihar Kano tun lokacin da Gwamna Abdullahi Ganduje ya nemi tsige Sarki Muhammdu Sanusi II (mai murabus) daga kan karagar Saurautar Kano, abin da ya jawo aka dakatar da mutum biyar daga cikin ‘yan majalisar.

Arewablog Data Bundle Ads

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

%d bloggers like this: