Biyan Kudin Jarrabawar Dalibai Ganduje Ya Cancanci Yabo


0 90

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Daga Anas Saminu Ja’en

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje a farkon makon nan ta biyawa daliban ‘yan asalin jihar Kano kudin jarrabawar Neco wadanda suka fadi jarrabawar Qualifying kuma kimanin dalibai dubu talatin da takwas da dari shida da talatin da biyu 38,632, suka rabauta da tsarin wanda kowane dalibi za a biya masa Naira dubu goma sha daya 11,000 wanda kimanin jimillar kudin shi ne Naira Miliyan dari hudu da ashirin da hudu da dubu dari tara da hamsin da biyu, kamar yadda Malam Muhammadu Garba kwamishin yada ya bayar da sanarwa.

Tabbas ya zama wajibi duk wani mai son ci gaban jihar Kano da kishin ilimin ‘ya’yan talawa ya yabawa mai girma gwamna Ganduje bisa namijin kokari da ya yi ya nuna shi dattijo ne, a matsayin sa na mai son ganin harkar ilimi ta inganta a fadin jihar nan wanda kowa yasan yadda ilimi ya ke baya kawo yau a lokacin da al’umma suke fama da karancin kudade ga bukatu sun yi yawa gwamna Ganduje yaga ya dace ya saukakawa al’umma tare da dauke musu biyan wannan kudaden karatun ‘ya’yan su wanda ya zuwa yanzu haka hukumar shirya jarabawar kammala Sakandare ta kasa wato NECO take gudanar da rijistar dalibai da za su rubuta jarabawan a wannan shekara ta 2019, inda nan take gwamnan ya ba da umarnin fitar da kudi domin biya wa kafatanin daliban jihar da ke karatu a makarantun sakandare na gwamnati a fadin jihar tare gargadin duk shugabannin makarantun da su guji karban kudi daga dalibai domin basu sakamakon jarabawar su.

Wasu Abubuwan Masu Alaka
1 of 607

- Advertisement -

Kafin wannan gwamna Ganduje ya ce ilimin ‘ya’ya mata a daukacin makarantun sakandire kyauta ne, Abun jin dadin shi ne gwamna ya ce wannan kunshin gwamnatin da zai yi a karo na biyu da matasa zai tafi.

Wannan abu da aka yi yasa al’umma farin ciki musamman iyayen yara da basu da halin biya kuma daman haka ya kamata a ce mutane sun yi su nuna farin cikin su a duk lokacin da aka ce abun alkairi ya same su, wanda lamarin biyan kudin makaranta ya shafi kowa koma adawa mutum yake yi abun zai shafe shi domin abu ne daya shafi miliyoyin mutane Kano. hakan yara nunawa duniya cewar gwamna Ganduje ya cika dattijon mai fada da cikawa tare da daukar shawara wanda haka ake son jagora nagari abun koyi, da wannan muke fatan nan gaba da yardar Allah a jihar Kano sai harkar ilimi ta yi fintinkau a fadin Najeriya kuma muna kira ga mai girma gwamna da hukumar ilimin jihar cewar su kara saka idanu akan harkar ilimi domin dawo da martabar ilimi ta hanyar samar da kwararrun malamai kuma masu kishi da son ci gaban jihar mu masu karo karatu a tura su tare da sabunta duk wani abu da ya shafi ilimi a samar da kyawawan muhallan koyo da koyarwa a fadin makarantun jihar Kano.

A karke ya kamata mutane masu amfani da kafofin sadarwa da sauran gidajan rediyoyi dana talabijin da ‘yan jaridu da ‘yan siyasa masu kishi a fadin kasar nan baki daya, da muji tsoron Allah wajan bayana duk alkairi ga dukkan wanda ya yi a fada sabanin a tsaya waje gudana ana son lallai sai an aibata wani ko wata ya dace a ringa ajiye banbancin siyasa musaka ci gaban yankin mu da jihohin mu dama kasar mu baki daya, duk wanda baya na’am da wannan abun alkairi da Ganduje ya yi to tabbas ba masoyin jihar Kano da ci gaban ta bane Allah ya ci gaba da shiga cikin lamarin shugabannin mu su ci gaban da kawomana aiyukan alkairi.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

-Business Advert-

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.