Labarai

BINCIKE: Yadda Yakubu Dogara Da UBEC Suka Yi Babakere Da Naira Bilyan Daya Na Gina Makarantu

Bincike ya nuna cewa a shekaru uku da suka gabata, hukumar ilmi ta UBEC ta fitar da naira milyan 97 ga wasu kamfanonin domin gina sabbi da sabunta makarantu a mazabar tsohon kakakin majalisar tarayya, Yakubu Dogara dake jihar Bauchi.

Kudin na daga cikin naira bilyan daya na gudanar da ayyuka a mazabar Yakubu Dogara.

Quickfix Property Limited, Delta Force limited da Maridiq Nigeria Limited sune suka karbi kudin kwangilar ginawa da sabunta makarantun a yankin, kamar yadda majiyarmu ta Budeshi ta bayyana.

A Kwalejin fasaha ta Gwamnati dake garin Tafawa Balewa, babu wani aiki guda daya da aka gudanar duk da cewa makarantar tana daya daga cikin wadanda ya kamata a yi wa aiki.

Shugaban makarantar, Mista Jatau Daniel ya bayyanawa majiyar mu ta Wikki Times cewa shekaru da dama an yi watsi da makarantar, inda ya kara da cewa bai san da cewa makarantar tana daga cikin makarantun da za su amfana da kudin mazabar da aka bayar ba.

Saidai ba iya kwalejin fasaha dake garin Tafawa Balewa kadai ba ce ba ta amfana da kudin ba. Domin binciken Wikki Times ya nuna cewa sauran makarantun da aka ware kudin domin su, ba su amfana yadda ya kamata ba, inda wasun su aka yi musu takaitaccen aiki wasu kuma ko oho.

Kwalejin na Tafawa Balewa wanda aka gina a shekarar 1978, shi kadai ne kwalejin fasaha dake mazabar ta Dogara, amma har yanzu babu abubuwan ci gaban da aka samar a makarantar, inda dalibai sama da 1400 suke fama da karancin kayayyakin koyarwa.

Shugaban makarantar ya kara da cewa gini na karshe da aka yi makarantar an yi shine shekaru ashirin da suka gabata, sai kuma ayyukan sabunta gine-gine da kungiyar iyayen yara da malamai (PTA) suke yi.

“Na samu damar ganawa da Yakubu Dogara a shekarar da ta gabata, inda na zayyano masa matsalolin da muke fuskanta a makarantar da kuma yadda makarantar take dab da rugujewa saboda gininta ya tsufa. Bayan ya karbi bukatun namu, ba mu sake ji daga gare shi ba, duk da cewa ya fada mana cewa zai waiwaye mu ba da jimawa ba”, cewar Mista Daniel.

Dalibai dai na fama da matsalolin da suka shafi rashin kyawun gini, rashin ababen zama, rashin kayan karatu da makamantansu duk da cewa makarantar na daga cikin makarantun da aka fitar da kudi domin yi wa aiki a cikin kudin mazabun da aka bayar. Haka kuma daliban sun koka da rashin wasu malaman darrusan da ake koya musu saboda karancin kayan aiki.

Haka wata makarantar firamare ma dake yankin kwalejin fasahar mai suna Central primary school tana daga cikin makarantun da ya kamata a ce sun amfana da kudin, amma ita ma babu wani gini da aka yi a cikinta.

Ajujuwa guda biyu da aka gina a makarantar an gina su ne a shekarar 2016 a karkashin shirin hukumar SDG. Duk da cewa a shekarar 2018 an bada kwangilar gina ajujuwa uku ga kamfanin kwangila na Maridiq Nigeria Limited, wanda kuma sune aka baiwa naira milyan 19 kudin kwangilar gudanar da ayyuka a kwalejin fasaha ta Tafawa Balewa.

Haka ita ma makarantar firamare ta Nahuta dake Tafawa Balewa ita ma an soma aikin amma ba a kammala ba aka yi wasti da su.

Ita ma wata makarantar karamar sakandire ta gwamnati dake bakin titi kilomita kadan bayan an baro garin Bogoro, kamfanin Quickfix ya gina ajujuwa uku ba tare da an samar da kayayyakin karatu ba.

Rahotanni sun nuna cewa dai, ko a Gwarangah mahaifar Dogara, suna karancin ababen more rayuwa da dama duk kasancewar sa ya haura sama da shekaru sha bakwai yana majalisar tarayya. Domin mahaifar tasa tana fama da matsalar hanyoyi, wutar lantarki, ruwan sha, ingantattun makarantu da sauran ababen more rayuwa.

Related Articles

One Comment

  1. Your copied and translated an investigative report by wikki times sponsored by national endowment for democracy without acknowledging either the investigative reporter or the sponsor. This is unethical and unprofessional. You are by this comment required to the right thing by either acknowledging them or deletethe story entirely from your database. Failure to do so within 48hrs will necessitate wikki times take action against you.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: