Rahoton Daily Trust
A yayin daya rage saura kwanaki hudu a gudanar da zaben gwamnonin Najeriya, wasu alkalumma da aka samu daga binciken masana sun nuna wasu gwamnonin Najeriya da ake ganin zasu kai bantensu a zabe, inji rahoton jaridar Daily Trust.
Majiyarmu ta ruwaito na gaba gaba a cikin wadannan gwamnoni shine gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jahar Kano
Wata kungiya mai zaman kanta, ANAP Foundation ce ta gudanar da wannan bincike, kungiyar ta kwashe tsawon shekaru tana gudanar da bincike akan zabukan Najeriya, tun daga shekarar 2011, inda tace tana yin hakan ne don ta samar da shugabanci nagari.
- Advertisement -
Alkalumman sun nuna cewa Ganduje zai bawa takarar gwamnan jahar Kano na jam’iyyar PDP, Injiniya Abba Kabir Yusuf tazara mai nisa , kuma Gandujen zai kai bantensa.
Daga cikin sakamakon da binciken ya bankado shine akwai wani kaso na jama’ar Kano dake goyon bayan Ganduje da suka hada da mata da suka amfana da tallafi kashi 21%, wadanda suka aminta dashi 17%, masu son ya zarce 17%, tallafi na matasa 11% da kuma wadanda suka gamsu da aikinsa 9%.
Sai dai a daya hannun, su kuma masu son Abba sun hada da masu son ganin an canza gwamnati 20%, wadanda Abba ke burgesu 25%, zabin farko 20%, masu sonshi 9% da kuma wadanda suke ganin yana da hazaka 5%.