Labarai

BINCIKE: Jiragen Sama Ne Ke Wurgawa ‘Yan Bindiga Makamai Da Abinci A Jihar Zamfara

Daga Comr Abba Sani Pantami

Jiragen sama da ke samar da makamai tare da abinci ga ‘yan bindiga shine babban dalilin da ya sa gwamnatin tarayya ta hana jiragen sama bi ta jihar Zamfara, an gano hakan a ranar Laraba.

Baya ga haka, ana amfani da jiragen saman wurin safarar zinarin da aka haka ba bisa ka’ida ba a jihar.

Gwamnatiin tarayya ta haramtawa jiragen sama bi ta jihar Zamfara a ranar Talata bayan taron da aka yi na tsaron kasa.

Ta kara da haramta dukkan hakar ma’adanai na jihar har sai baba ta gani, kamar yadda Jaridar The Nation ta ruwaito.

Majiyoyin tsaro masu yawa a jiya sun bayyana cewa: “Akwai bayanan sirri masu tarin yawa da suke sanar da cewa ‘yan bindiga na samun makamai daga jiragen sama.

“Ganin cewa dukkan jihar Zamfara a rufe take yasa wannan bayanin sirrin ya tabbata. Hana wucewar jiragen sama ta jihar ne zai dakile ‘yan bindigan sannan dakarun soji su shiga su fitar dasu.”

Wannan hukuncin saboda tsaro ne kadai ba siyasa tasa aka yanke shi. An yanke shi ne domin inganta tsaron jihar da yankin baki daya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Back to top button
%d bloggers like this: