Daga Comr Abba Sani Pantami
Kasar Nijeriya na daya daga cikin manyan kasashe a nahiyar Afirka kuma tana da mutane fiye da miliyan 200.
Akwai jihohi 36 a kasar da babban birnin tarayya Abuja.
Domin gano jihar da ta fi arziki a Nijeriya, yana da muhimmanci a duba alkalluman karfin tattalin arzikin cikin gida wanda ya kunshi dukkan cinikayya na jihar wato GDP.
Ga jerin jihohi 10 da suka fi arziki a Nigeria kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
1. Lagos – $33.68 biliyan
Legas ce kan gaba cikin jerin jihohin da suka fi arziki a Nigeria. Ita ce jihar da ta fi saura cigaba.
Jihar na da fadin kasa na sakwaya kilomita 3,577 da GDP na $33.68 biliyan.
2. Rivers – $21.17 biliyan
Rivers na daya daga cikin jihohi masu arziki a Nigeria. Tana da fadin kasa na Sakwaya kilomita 11,077.
Yawan jama’ar jihar ya kai miliyan 5.2 sannan GDP dinta $21.17 biliyan. Jihar ce kan gaba wurin albarkatun man fetur da gas.
3. Delta – $16.75 biliyan
Jihar Delta na yankin kudancin Nigeria, tana da yawan mutane da suka kai miliyan 4.1. GDP na jihar ya kai $16.75 biliyan.
Jihar na da man fetur da gas da albarkatun kasa kama kaolin, lignite, silica sa sauransu.
4. Oyo – $16.75 biliyan
Jihar Oyo na yankin Kudu maso Yammacin Nigeria. Adadin mutanen jihar ya kai miliyan shida. GDP na jihar $16.12 biliyan.
Jihar na noman kayayyaki kamar shinkafa, doya, masara, cocoa, man ja, gero da sauransu.
5. Imo – $14.21 biliyan
Imo jiha ce da ke yankin Kudu maso Gabashin Nigeria. GDP na jihar $14.21 biliyan.
Imo na da albarkatu da suka hada da man fetur, iskar gas, zinc, lead da sauransu. Manyan kamfanonin man fetur a jihar sun hada a Agip, Royal Dutch Shell, Chevron Corporation.
6. Kano – $12.39 biliyan
Yawan mutane da ke jihar Kano sun kai kimanin miliyan 11 sannan GDP na jihar ya kai $12.39 biliyan.
Kano ta yi fice wurin samar da fatar dabobi domin sarrafa abubuwa da dama da noman auduga, wanken soya, ridi, tafarnuwa da sauransu.
7. Edo – $11.89 biliyan
Benin City ne babban birnin jihar Edo. Yawan mutanen jihar ya kai miliyan 3.5 da GDP na $11.89 biliyan.
8. Akwa Ibom – $11 biliyan
Akwa Ibom jiha ce da ke Kudancin Nigeria.Tana da yawan mutane da suka kai miliyan 5.5. Kabilun da suka fi yawa a jihar sun hada da Ibibio, Annang, Oron, Eket da Obolo. GDP din ta ya kai $11 biliyan.
9. Ogun – $11 biliyan
Ogun na yankin kudu maso yammacin Nigeria, Yawan mutanen jihar ya kai miliyan hudu.
Akwai manyan kamfanoni da yawa a jihar kamar kamfanin simintin Dangote, kamfanin simintin Lafarage da sauransu. GDP na jihar $11 biliyan.
10. Kaduna – $10.33 biliyan
Kaduna jiha ce da ke yankin Arewa maso Yamma, Yawan mutanen jihar sun kai miliyan 6.1. Akwai kabilu da dama a jihar. GDP na jihar ya kai $10.33 biliyan.